Majalisar Kasa Ta Musanta Zargin Yin Cushe A Cikin Kasafin Kudi

Majalisar dokokin Najeriya ta ce babu gaskiya a zargin cewa ta yi chushe a kwarya-kwaryar kasafin kudi na Naira biliyan 819.5 da aka amince da shi, inda ta kasafta yadda za’a raba kudin da a ciki majalisar za ta sami Naira biliyan 70 domin sayen motoci da kayan aiki na shekaru hudu masu zuwa.

Hakan ya bayyana ne a daidai lokacin da mai tsawatarwa na masu rinjaye a majalisar dattawa Mohammed Ali Ndume ya jaddada cewa zartar da dokar karin kudin na daga cikin aiyukan da kundin tsarin mulki ya tanadar wa Majalisar.

Ndume ya ce batun Naira biliyan 500 da shugaban kasa ya nema daban ya ke da Naira biliyan 70 da aka ware wa ‘yan majalisa a kasafin kudin wannan shekara da muke ciki.

Ndume ya ce tun da aka koma tafarkin dimokradiya a 1999 ake yin irin wanan tsarin domin da motoci ‘yan Majalisa ke kai ziyara mazabunsu, sannan kuma duk kayan aikin da suke nema domin gudanar da ayukan majalisar ana tanadin su.

Ndume ya ce “kuma wadannan kudaden ne aka ware wa yan Majalisa a kasafin kudin bana. Farashin kaiyayyaki ne ke ta hawa a kasar, saboda motar miliyan 10 a yan shekarun baya, yanzu Naira miliyan 30 ake sayar da ita, shinkafa ma a da Naira dubu 8 ake sayar da ita amma yanzu shikafa ta kai dubu 40, haka buhun Masara a wasu wurare, saboda haka ba daidai ba ne a ce za’a ba yan majalisa wani kudi kyauta daga bangaren gwamnati ko na hasafi, sai dai na aiyuka da doka ta tanadar.”

Shi kuwa dan Majalisa mai Wakiltan Gwaram a JIhar Jigawa Yusuf Shittu Galambi ya yi ishara ga rahottani da ke nuna cewa an ware kudaden ne don samar da ofisoshin ‘yan majalisa da kuma gyara harabar majalisar.

Yace “akwai hukumar gudanar da majalisar da ta ke tafiyar da kudaden gyara ba ‘yan majalisa ba. An san za’a samI sabuwar majalisa a wannan shekara saboda haka tuni aka ware mata kudi a kasafin shekara 2023.”

Galambi ya ce ba zai so su shiga cikin wani cece-kuce kan wani kaso da za’a ba ‘yan majalisa Naira biliyan 70 kyauta ce ba. Ya bayyana bacin ran sa kan yadda wasu yan jaridu ba sa bincike kafin su saki labari, inda ya kalubalance su da su rika bin diddigin labari kafin a yayata shi.

Masanin harkokin gudanar da mulki Aminu Jumare yayi tsokaci kan wannan batu cewa “ya kamata ‘yan majalisa su ciza su hura domin a sami sauki a kasa, ganin cewa ana wahala kan batun karin kudin man fetur dama cire tallafin da aka yi.”

Aminu ya ce ‘yan majalisa su hakura a yi amfani da kudaden nasu wajen sayen motoci na sufuri, alabasshi bayan wani lokaci mai tsawo suna iya neman kudin su.

Manazarta na cewa mai yiwuwa ne shugaban kasa ya sake duba lamarin da idon basira, ya janye kudaden da za’a ba yan majalisar, kamar yadda ya ce za’a sake duba batun raba Naira dubu takwas takwas ga ‘yan kasa miliyan 12 a matsayin tallafi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply