Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Majalisar Dokokin Kaduna Ta Zayyano Manyan Zunubban El-Rufa’i A Mulki

IMG 20230808 WA0052(1)

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta ce ta fara gudanar da bincike kan yadda tsohon gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufai ya kar?o tare da tafiyar da basuka na tsawon shekaru takwas da ya yi yana mulkin jihar.

A baya-bayan nan ne dai gwamnan jihar mai ci Malam Uba Sani ya ?ara cewa gwamnatin nasa ba ta iya gudanar da wasu muhimman abubuwa na yau da kullum da suka ha?a da biyan ma’aikata albashi sakamakon tarin bashin da ke kan jihar.

Wasu al?aluma da hukumar da ke gudanar da harkokin bashi a Najeriya ta fitar, sun nuna cewa Kaduna ce jiha ta biyu da bashi ya yi wa katutu bayan jihar Lagos a Najeriya.

Majalisar ta bakin shugaban kwamitin da ke jagorantar binciken ta ce lamarin zai iya kai wa ga neman tsohon gwamnan, Nasir El-rufai ya gurfana a gaban majalisar.

?aya daga cikin ‘yan majalisar jihar ta Kaduna kuma mamba a kwamitin da ke wannan bincike, Hon Alhassan Mohammed Ikara ya ce :
“Gwamnatin da ta shu?e ta ciyo basuka da yawa domin gudanar da ayyukan raya ?asa. To amma bayan da ta wuce sai mu ka ga ta tafi ta bar baya da ?ura domin wa?annan basuka sun bar baya da ?ura inda yanzu a halin da ake ciki gwamnatin jihar Kaduna ba ta iya biyan albashi har sai an ci bashi.” In ji Hon Alhassan.

Da aka tambayi Hon Alhassan kan cewa me ya sa wasunsu da suka kasance a majalisar lokacin gwamnatin tsohon gwamnan ba su hana ba? Sai ya ce
“Ai yanzu ne ake cire basukan da gwamnatin ta baya ta ciyo. To shi ya sa duk muke da damuwa a kan wancan bashi da aka ciyo.” In ji Hon Alhassan.

Hon Alhassan Mohammed Ikara ya ce ba wani abu ba ne ya sa muke son ?addamar da wannan bincike illa domin “muna son sanin wasu abubuwa guda hu?u”.

Na farko shi ne ko an bi ?a’ida wajen bashin da aka ciyo?
Da kuma aka ciyo bashin ko an yi abin da doka ta tanadar kamar kai wa majalisa ta sahale wa gwamnati cin bashin?

Na uku aikace-aikacen da aka kar?o bashin domin yi su ne aka yi?

Na hu?u za ka ga ‘yan kwangilar da suka yi aikin har yanzu suna bin ku?a?e kuma ayyukan hanyoyin sun tsaya ba a gama ba.

Hon Alhassan ya ?ara da cewa “idan ka kalli ku?a?en da ‘yan kwangila suke bi sun haura naira biliyan 120. Saboda haka idan gayyata ta kai ga tsohon gwamna ba laifi ba ne amma yanzu dai mu?arrabansa muke gayyata domin su mana bayani kan yadda aka ciyo bashi da yadda aka kashe ku?a?en.

Exit mobile version