Majalisar Dokokin Jihar Kano Za Ta Yi Wa Dokar Masarautu Gyara

IMG 20240229 WA0298

Majalisar Dokokin Kano ta amince a dawo da dokar masarautu ta jihar domin yi mata kwaskwarima.

Majalisar ta amince da hakan ne a zaman da ta yi a ranar Talata.

A shekarar 2019 gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta yi wa dokar masarautu ta jihar gyara inda aka ?ir?iro ?arin masarautu gudu hu?u masu daraja ta ?aya.

Masarautun sun ha?a da Gaya da ?araye da Rano wa?anda aka ?aga darajarsu zuwa masu daraja da ta ?aya daidai da masarautar Kano.

Sai kuma Masarautar Bichi da aka ?ir?iro, abin da ya sa Kano ta zama tana da masarautu biyar masu daraja ta ?aya.

Masu adawa da matakin a lokacin sun soki ?ir?iro sababbin masarautu a Kano domin a cewarsu hakan zai rusa tarihin masaratuar Kano na daruruwan shekaru, inda masarautar take da ?ima a idon duniya saboda fa?inta da kuma tasirinta.

Amma mutanen yankunan da aka ?ir?iro wa masarautun sun yi maraba da matakin, suna cewa hakan zai ?ara kawo musu ci gaba da bun?asa.

Related posts

Leave a Comment