Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya tare da hadin gwiwar ma’akatar kudi da tsare-tsare suka kira taron gaggawa a kan yanayin da ake ciki, inda aka cimma matsayar hadin gwiwa da dukan masu ruwa da tsaki a kasar don samo mafita mai dorewa kan matsalar karancin abinci.
Hakan ya zo ne kasa da mako guda da ayyana dokar ta-baci a fannin samar da abinci a yayin da hauhawar farashin kayayyaki ya sanya wasu da dama suka kasa samun saukin abinci tare da kara yawan karancin abinci mai gina jiki a kasar da gwamnatin Najeriya ta yi.
Taron da ya gudana a birnin tarayya Abuja dai ya cimma wannan matsayar hadin gwiwa tsakanin dukan masu ruwa da tsaki ne don samar da mafita mai dorewa a daidai lokacin da karin farashin kowacce litar mai ya tsananta hauhawar farashin kayayyaki daga ranar Talatar nan inda jiga-jigai da suka halarci taron suka yi kira ga dukkan ‘yan kasa da su bada mahimmanci ga shiga aikin gona gadan-gadan su rika shuka a bisa kashin kai don samar da wadataccen abinci da kan su don rage matsalar karancin abinci da yunwa.
Shubra Mahmud wadda ta wakilci babban sakataren ma’aikatar noma da raya karkara na tarayyar Najeriya, ta bayyana cewa kasar na cikin wani hali na matsalar abinci amma gwamnatin tarayya ta riga ta bada umarnin a dauki matakan gaggawa wajen kawo karshen hakan daga dukan masu ruwa da tsaki.
Shubra Mahmud ta kara da cewa ganin yadda mata ke kan gaba a fannin aikin gona tuni ma’aikatar noma da raya karkara ta sanya su a kan gaba a dukan hidimominta don karfafa aikinsu a samo mafita ga matsalar noma.
A wani bangare kuma wakilin ofishin asusun Tallafawa Noma na Duniya a Najeriya, Dede Ahoefa Ekoue wanda aka wakilta a yayin taron, ya yi kira ga dukan masu ruwa da tsaki su dauki matakan gaggawa don shawo kan matasalar karancın abinci.
Ekoue yana mai cewa asusun IFAD na da yakinin cewa idan aka dauki matakan hadin gwiwa aka kawo hukumomin gwamnati, manoma, ‘yan kasa masu bukatar kayan abincin da kuma saura masu ruwa da tsaki yana da mahimmanci wajen gina tsarin samar da abinci mai dorewa tare da cewa wani bangare daya tilo ba zai iya cimma nasara a samar da wadataccen abinci ga ‘yan kasar ba.
Shi ma Darakta kuma wakilin ofishin shirin samar da abinci kasa da kasa na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, David Stevenson ya ce, ana buƙatar yin aiki tukuru kuma ofishinsa ya na magana da masu ruwa da tsaki a duk fadin Najeriya a kan batun bayar da shawarwari a game da kawar da matsalar yunwa gaba daya tare da tabbatar da cewa an habaka ci gaban da aka samu a yanzu.
Stevenson ya kara da cewa masu ruwa da tsaki su marawa juna baya don yin iya bakin kokarinsu a inganta abubuwa da gina dogaro da kai a fannin samar da abinci.
Tun bayan cire tallafin man fetur a karshen watan Mayun da shugaba Tinubu ya yi jim kadan bayan karbar rantsuwar kama aiki ne farashin kayayyakin abinci ya yi tashin gwauron zabi, inda gwamnatin ta ce zata yi amfani da wadannan kudaden tallafin wajen inganta fannin aikin noma da kuma samar da taki da hatsi ga manoma da gidaje masu fama da tsadar kayayyakin masarufi.