Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Nemi A Saki Wanda Ya Yi Ɓatanci Ga Annabi

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci Nijeriya da ta saki mawakin da aka yankewa hukuncin kisa saboda zarginsa da batanci ga Annabi Muhammad (SAW) ba tare da wani ɓata lokaci ba.

A watan da ya gabata ne wata kotun shari’a a Kano, ta yankewa Yahaya Aminu Sharif hukuncin kisa, bayan da ya yi wakar batanci ga Musulunci da Annabi, kuma ya raba a dandalin sada zumunta na WhatsApp.

A cikin wata sanarwar hadin guiwa da Majalisar Dinkin Duniya suka fitar, sun bayyana cewa “Waka ba laifi bace,” kuma suka bayyana cewa tun farko mawakin bai samu kwararrun lauyoyi ba ne.

Ita ma wata kwararra a kare hakkokin al’adun bil Adama, Karima Bennoune, ta bayyana cewa, sabawa dokar ‘yancin dan Adam ne yanke hukuncin kisa don an yi waka tare da raba ta a kafofin sadarwa.

Ta roki Nijeriya da ta janye wannan hukuncin kisan, kana ta tabbatar da tsaron lafiyar mawakin har zuwa lokacin da zai daukaka kara kan hukuncin.

Wasu Fusatattun mutane sun gudanar da zanga zanga bayan da Sherif ya yi wakar, inda suka kona gidan iyayensa a ranar 4 ga watan Maris.

Labarai Makamanta

Leave a Reply