Majalisa Za Ta Yi Dokar Haramta Wa Kotuna Kwace Kujerun Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni

Sabuwar dokar na son a sauya sashin kundin mulkin kasa wanda ya bada damar kwace kujerar shugaban kasa ko gwamna a kotu. Bukatar na son haramta kwace kujerar dukkan masu takara idan aka samu daya daga cikinsu ke da nakasa a takardun karatu.

Dokar na bukatar sauya kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, domin bai wa dan takarar shugaban kasa ko gwamna kariya wadanda abokan takararsu ke da matsala a takardun makaranta.

Bukatar ta bayyana a gaban majalisar ne ta hannun Solomon T. Bob dan Jam’iyyar PDP daga jihar Ribas. Bukatar tana son a sauya sashi na 142 sakin layi na 1.
Dokar ta ce matukar an zabi mutum a matsayin shugaban kasa, za a iya soke zabensa matukar akwai wata nakasa a takardun makarantun abokin takararsa da aka zabesu tare.

Sabuwar dokar tana son a sauya sashi na 142 na kundin tsarin mulkin inda za a iya kwace kujerar mataimakin kadai sannan a saka wani a maimakonsa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply