Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce nan ba da dadewa ba majalisar za ta ɗage dakatarwar da ta yi wa Sanata Abdul Ningi (PDP, Bauchi ta Tsakiya).
Hakan na zuwa ne sa’o’i 24 bayan sanatan ya rubuta wasiƙa ga Akpabio, inda ya yi barazanar daukar matakin shari’a idan ba a dage dakatarwar da aka yi masa ba cikin kwanaki 7.
An dakatar da Ningi ne biyo bayan zargin da ya yi cewa an yi cushen N3.7m a kasafin kudin shekarar 2024, kamar yadda kafafen watsa labarai suka ruwaito.
Bayan zazzafar muhawara da Sanatoci suka yi a zauren majalisa kan lamarin, an dakatar da Ningi na tsawon watanni uku tare da neman ya rubuta wasikar neman gafara.
Ningiya yi barazanar shiga kotu Sai dai a wata wasika da lauyansa, Femi Falana (SAN) ya rubuta, Ningi ya zargi Akpabio da zama alkali, wanda ake ƙara, da wanda ke a ƙara a kes ɗin, wanda ya saba kundin tsarin mulki.
Sanatan ya zargi Akpabio da sa a gurfanar da shi a gaban majalisar dattawa ranar 14 ga Maris, 2024 wanda ya saba wa tanade-tanaden dokokin majalisun dokoki 2018.
Amma da yake amsa tambayoyin ƴan jarida ranar Juma’a bayan ya dawo daga taron kungiyar ‘yan majalisa a birnin Geneva na kasar Switzerland, Akpabio ya ce nan ba da dadewa ba majalisar dattawa za ta sake nazari.
“Majalisa ta ɗauki matakin, ni ban ga takardar ba amma Sanata Ningi ɗaya daga cikinmu ne, menene dakatarwa? Ina da yaƙinin nan da ƴan kwanaki zai dawo cikinmu. “Saboda haka babu wata matsala, zamu warware lamarin cikin ruwan sanyi, mun ƴan gida ɗaya ne.”