Majalisa Ta Yi Watsi Da Bukatar Tinubu Na Tura Dakarun Soji Nijar

‘Yan Majalisar Dattawan Najeriya sun ƙi amincewa da buƙatar neman goyon bayansu da Shugaba Bola Tinubu ya aika kan tura sojojin ƙasar zuwa Nijar don tilasta wa sojoji komawa kan tsarin mulki.

Shugaba Tinubu ya nemi goyon bayan ‘yan majalisar ne cikin wata wasiƙa da ya aika musu ranar Juma’a, inda ya bayyana musu matakan da ya ɗauka a matsayinsa na shugaban ƙungiyar Ecowas ta raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma.

Bayan fitowa daga wani zaman sirri a ranar Asabar, Majalisar ta jaddada goyon bayanta ga yunƙurin Ecowas, ban da maganar amfani da ƙarfin soja.

“Mun ƙi amincewa saboda ba abu ne da ya kamata a fara tunaninsa ba ma, saboda abu ne na cikin gida,” kamar yadda Sanata Ali Nudme ya shaida wa BBC.

Sanatan ya ƙara da cewa shawarar da mafi yawan sanatocin suka bayar ita ce a ci gaba da yunƙurin sulhu ta hanyar difilomasiyya, maimakon ƙarfin soja.

“Muna da shugabannin ƙasa, waɗanda sojojin Nijar ke mutuntawa kamar Buhari da Abdulsalam da Babangida da Jonathan, idan aka yi amfani da waɗannan za a samu masalaha,” a cewarsa.

Cikin matakan da Tinubu ya ɗauka akwai kulle iyakokin Najeriya da Nijar, da katse wutar lantarkin ƙasar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply