Majalisa Ta Tabbatar Da Naɗin Jakadu

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan ya tabbatar da nadin jakadu 39 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika gaban majalisar.

Majalisar ta kuma amince da nadin Malam Suleiman Sani daga birnin tarayya a matsayin jakada.

Wannan tabbatarwan ya biyo bayan rahoton kwamitin majalisar kan harkokin waje wanda ya samu shugabancin, Sanata Adamu Bulkachuwa mai wakiltar mazabar Bauchi ta arewa.

A wata wasika da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura wa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce wannan nadin na biyayya ga sashi na 171 na kundun tsarin mulkin 1999 na Najeriya.

Bulkachuwa ya ce wasu daga cikin wadanda aka zaba din basu kasar nan amma an yi musu tantancewar ta yanar gizo. Ya ce an tambayesu a kan diflomasiyya da kuma alaka.

Ya yi bayanin cewa wadanda aka zaba daga jihohin Yobe da Neja an dakatar da su saboda matsalar da ke tattare da nadin.

Dan majalisar ya ce sauran mutum 39 da aka zaba sun amsa tambayoyi kuma an amince da nadin.

A wani bangare, Sanata Philip Aduda na jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar Birnin tarayya, ya zargi rashin saka kowa daga birnin tarayya a jerin sunayen jakadun.

Lawan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta fitar da kudi isassu a kan ayyukan da za ta turasu kasashen ketare.

Ya ce babu amfanin tura jama’a kasashen ketare kuma a ki wadata su da abinda ya dace. “Ko dai a basu isassun kudi da kulawar da ya kamata ko kuma a rage yawansu,” inji shi.

Jakadun da aka tabbatar sune;
Engr Umar Suleiman (Adamawa);
Kelvin Peter (Adamawa);
Chief Elejah Onyeagba (Anambra);
Farfesa Monique Ekpong (Cross River).
Ominyi N. Eze (Ebonyi);
Yamah Mohammed Musa (Edo);
Maj. Gen. C. O. Ugwu (Enugu);
Dr. Hajara I. Salim (Gombe);
Amb. Yahaya Lawal (Katsina);
Ademola Seriki (Lagos).
Cif Sarafa Tunji Ishola (Ogun);
Adejare Bello (Osun);
John Usanga (Akwa Ibom);
Hamisu Umar Takalmawa (Kano);
Philip Ikurusi (Bayelsa);
Hon. Tarzcor Terhemen (Benue).
Al-Bishir Ibrahim Al-Hussain (Borno);
Obiezu Ijeoma Chinyerem (Imo);
Ali M. Magashi (Jigawa);
Prof. M. A. Makarfi (Kaduna).

Sauran sune; Henry John Omaku (Nasarawa); Sadiya Ahmad Nuhu (Kano);
Adeshina Alege (Oyo);
Shehu Abdullahi Yibaikwai (Plateau);
Maureen Tamuno (Rivers),
Faruk Yabo (Sokoto).
Abubakar Moriki (Zamfara);
Adamu M. Hassan (Taraba);
Abubakar D. Ibrahim Siyi (Bauchi);
Paul Oga Adikwu (Benue);
Jazuli Imam Galadanci (Kano);
Dare Sunday Awoniyi (Kogi).
Ibrahim Kayode Laaro (Kwara),
Abioye Bello (Kwara);
Zara Maazu Umar (Kwara);
Mrs. Nimi Akinkugbe (Ondo);
Debo Adesina (Oyo);
Ms. Folakemi Akinyele (Oyo) da Oma Djebah (Delta).

Labarai Makamanta

Leave a Reply