Shugaban kwamitin sa ido kan harkokin rundunar soji a majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume ya ce kwamitin ha?aka na majalisar Dattawa kan harkokin tsaro da suka hada da na rundunar tsaro, sojin kasa, sojin ruwa da sojin sama za su fara tantance sabbin hafsoshin tsaron Nijeriya a cikin makon da zamu shiga.
Ndume ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai Abuja.
A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban majalisar dattijan Ahmad Lawan, ya mika bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari na amince da sabbin hafsoshin tsaron ga kwamitin ha?aka na majalisar dattijan da ya ha?a da kwamitin rundunar tsaro, sojin kasa, sojin sama da sojin ruwa, domin su yi kyakkyawan bincike.
Lawan ya ba kwamitin makonni biyu da su je su yi binciken su tare da maido masa da rahoto a yayin zaman majalisar.
Sabbin hafsoshin tsaron da aka na?a su ne: Manjo Janar Lucky Eluonye Onyenuchea Irabor a matsayin shugaban rundunar tsaro; Manjo Janar Ibrahim Attahiru (Hafsan rundunar sojin kasa); Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo (Hafsan rundunar sojin ruwa); da kuma Air Vice Marshal Isiaka O. Amao (Hafsan rundunar sojin sama).
Za su maye gurbin tsofaffin hafsoshin tsaron da suka hada da Janar Abayomi ( shugaban rundunar tsaro); Laftanar Janar Tukur Buratai (Hafsan rundunar sojin kasa); Vice Admiral Ibok Ete Ibas (Hafsan rundunar sojin ruwa) da Air Vice Marshal Sadique Abubakar (Hafsan rundunar sojin sama).
Yayin amsa tambayoyi, Ndume ya ce: “Bai kamata a tantance hafsoshin tsaron a bainar jama’a ba. “Idan ka yi hakan to kamar kana nufin za ka kawo tarnaki wa tsaron kasa musamman ma idan akwai al’amuran da ke faruwa na damuwa ga tsaron kasar.”
Ya ce kwamitin hadakar zai tantance sabbin hafsoshin tsaron a cikin wannan makon tunda dai makonni biyu kawai a ka ba kwamitin.