Majalisa Ta Ki Amincewa Da Nadin El Rufai A Matsayin Minista

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa majalisar Dattawa ta ƙi tabbatar da tsohon Gwamnan Kaduna a matsayin minista kamar yadda Shugaba Tinubu ya nema.

Sauran mutum biyu da majalisar ba ta tabbatar ba su ne Sani Abubakar Danladi daga jihar Taraba, da kuma Stella Okotete ta jihar Delta.

Shugaban Majalisa Godswill Akpabio ya ce suna jiran rahoton jami’an tsaro kafin su tabbatar da mutanen uku.

Su kaɗai ne ba su shiga cikin mutum 45 ba da majalisar ta tabbatar a yau Litinin, amma ta tantance su tun daga Litinin da ta gabata da suka fara zaman.

Labarai Makamanta

Leave a Reply