Majalisa Ta Bukaci Tinubu Ya Hukunta Masu Hannu A Damfarar Jirgin Nigeria Air

Majalisar wakilai ta tarayya ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya kafa kwamiti domin gudanar da bincike mai zurfi kan yadda aka gudanar da aikin farfado da jirgin sama na Nigerian Air.

Nnolim Nnaji da ke jagorantar kwamitin kula da harkokin sufurin jiragen sama na majalisar wakilan ne ya gabatar da bukatar daukar matakin a Abuja, bayan nazarin da ya kammala akan lamuran da suka shafi jirgin saman.

Kwamitin ya kuma bukaci a gurfanar tare da hukunta dukkanin jami’an da suke da hannu a shirin kaddamar da jirgin da yayi batan dabo, jim kadan bayan gabatar da shi, lamarin da ‘yan majalisar suka bayyana a matsayin damfara.

Kwamitin ya bayyana rashin gamsuwa da ayyukan tsohon ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ne a ranar Talatar da ta gabata, yayin sauraron bayanan wasu jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki da suka bayyana gabansa domin bayar da bahasi, akan abinda suke da masaniya akai.

Bayan shan matsin lamba daga majalisun Najeriya da kuma daidaikun al’umma mukaddashin babban manajan kamfanin jiragen sama Kaftin Dapo Olumide ya ce ba shakka sun yi amfani da jirgin Ethiopian Air ne wajen gabatar da jirgin sama na Nigerian Air.

Tun a ranar 26 ga watan Mayun da ya gabata, cece-kuce ya biyo bayan gabatar da jirgin na Nigerian Air bayan da aka gano cewar jirgin na Ethiopian Air ne amma aka lallube rubutun da ke nuna alamun kamfanin.

Sai dai manajan ya ce kai tsaye matakin na su na wancan lokaci na nufin kaddamar da suna ko kuma tambarin jirgin na Nigeria Air ne ba wai jirgin kai tsaye ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply