Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar a ranar Talatan nan, majalisar wakilan tarayya ta bu?aci Ministar jin kai, Hajiya Sadiya Umar Farouk, ta sauka daga mu?aminta idan bata shirya aikin da ya dace ba.
An ruwaito cewa hakan ya biyo bayan gazawarta a lokuta da dama na bayyana a gaban Kwamitocin majalisar domin kare kasafin ku?in ma’aikatarta.
Muktar Betara, shugaban kwamitin kasafin Ku?i a majalisar shi ne ya fa?i haka yayin zaman bincike kan kutsen biliyan N206bn a kasafin ku?in 2023 daga ma’aikatar jin ?ai da walwala.
Kamfanin dillancin labarai na ?asa (NAN) ta ruwaito cewa ma’aikatar ta ware wa aikin raba ragar sauro Biliyan N206,242,395,000 kuma Bankin duniya ne ke ?aukar nauyin shirin.
Shugaban kwamitin, Hon. Betara, wanda ya nuna fushinsa a fili ya kalubalanci cewa me yasa Ministar ta gaza zuwa ta kare sanya ku?in, inda ya kara da cewa idan bata shirya ba ta aje aiki. “Duk lokacin da Kwamiti ya gayyaci ministar ba ta zuwa. Idan bata shirya aiki ba ya kamata ta sauka kawai.”
Da take bayanin inda aka samu kuskuren tun farko, Minista kudi, Hajiya Zainab Ahmed, tace an cusa abun ne tun a Ofishin Kasafi. Tace ya kamata ace Ministan jin ?ai ta ankarar da Ofishin kamar yadda takwarorinta suka yi.
Zainab Ahmed tace ma’aikatar tsaro, ma’aikatar makamashi da sauran ma’aikatun gwamnatin tarayya duk sun tafka kuskure amma suka garzaya aka gyara.