Rahotanni daga Majalisar wakilai ta tarayya Abuja na bayyana cewar ‘yan majalisar wakilai sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ?age kidayar jama’a da gidaje data shirya yi a shekarar 2021, nan take ba tare da ?ata lokaci ba.
Wannan kiran yazo ne bayan zauren majalisar ya kar?i kudirin ?asa wanda ?an majalisa mai wakiltar maza?ar Bosso/Paikoro a majalisar wakilai ta ?asa daga jihar Neja, Shehu Beji, ya gabatar mata a zaman ta na ranar Laraba.
Yayin da yake gabatar da kudirin, ?an majalisar yace, akwai dalilai da dama da zasu sa a dakatar da shirin kidayar wa?anda zasu shafi sakamakon da za’a samu bayan an kammala.
Ya ?ara da cewa samun nasarar wannan aikin na ?idaya zai samu tasgaro sosai saboda matsalar tsaron da ‘yan Najeriya ke ciki a sassa daban-daban na ?asar nan.
“Kodai wasu an tilasta musu barin matsugunin su ko kuma an kassara musu rayuwarsu ta yau da kullum.” inji shi. Sannan kuma Beji ya bayyana cewa babu tabbas ?in masu ?idayar zasu samu ingantaccen tsaro a mafi yawancin sassan ?asar nan da matsalar tsaro ta shafa.