Magu Ya Samu Babban Matsayi A Hukumar ‘Yan Sanda

Rundunar ‘Yan Sanda ta ƙasa ta sanar da ƙarin girms da ta yi wa wasu manyan jami’an ta su 18 a ranar juma’a.

Daga cikin wadanda suka samu ƙarin girman sun haɗa da muƙaddashin shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC Ibrahim Magu, inda ya zama cikkaken Kwamishinan ‘yan sanda dags matsayin da yake akai na mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda.

Shugaban kasa Buhari ne ya naɗa Magu shugabancin Hukumar a shekarar 2015, duk da ƙin amincewa da tabbatar da naɗin nashi da majalisa ta yi, Buhari bai sauya matsayin shi akai ba.

Sanarwar ƙarin girman na ƙunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da ta samu sanya hannun jami’in hulda da jama’a na Hukumar Ikechukwu Ani.

A baya bayan nan dai Magu ya fuskanci wasu tuhume tuhume da ministan shari’a Abubakar Malami ya gabatar a kanshi, lamarin da ya kai aka tsare Magu sannan da dakatar dashi daga shugabancin Hukumar ta EFCC.

Labarai Makamanta

Leave a Reply