Maganin Talauci: Ya Kamata Kowane Dan Najeriya Ya Koma Noma – Uwargidan Shugaban Kasa

IMG 20240228 WA0024(1)

Uwargidan shugaban ƙasa Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su tashi don ƙara shiga harkar noma, inda ta ce ƙasar za ta iya samarwa kanta isasshen abinci.

Remi ta faɗi haka ne a lokacin da ta karɓi bakuncin mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina Mohammed a ofishinta ranar Laraba a fadar gwamnati da ke Abuja.

Uwargidan shugaban ƙasar ta bayyana cewa, ɓullo da shirye-shirye dban-daban da gidauniyarta ta Renewed Hope Initiative ta yi, musamman a fannin noma, samar da aikin yi, ilimi, lafiya da jin daɗin jama’a, duka ta yi shi ne don ƙara karfafa irin ƙoƙari da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke yi.

“Shugaban ƙasa ya ɗauki matakan da suka dace. Waɗannan matakai za su taimaka mana wajen gina Najeriya. Ya kamata mu zama masu gaskiya dangane da albarkatun da Allah ya ba mu,” in ji Remi.

Ta kuma nanata buƙatar zaburar da matasa wajen yin tunanin da ya dace a kan ƙasar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply