Mafita Guda Da Ta Rage Wa ‘Yan Najeriya Ita Ce Rungumar Noma – Shugaba Tinubu

IMG 20240225 WA0030

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa fadar Shugaban Kasa ta yi kira ga ‘yan Najeriya su rungumi noma gadan-gadan don magance tashin farashin kayan abinci da ake fuskanta a kasar.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ne ya yi wannan kiran yayin taron da ya yi da wata kungiyar editocin yanar gizo ta ACOE a Abuja.

Shugaban kungiyar ACOE, Martins Odiete ne ya fitar da sanarwar bayanan Bayo a taron manema labarai da ya yi a ranar Asabar a Abuja.

A cewarsa: “A shekarar 1976, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kaddamar da shirin ‘Operation Feed the Nation,’ don karfafa aikin gona. “A shekarar 1984, lokacin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hau mulki, akwai karancin shinkafa, madara, da sukari, sai gwamnati ta bude gidajen ajiya don samar da wadannan kayan ga jama’a.

“Wannan ba shi ne karon farko da muke fuskantar irin wannan kalubalen ba. “Gwamnati na zuba jari a harkar noma domin samar da abinci mai araha, kuma a matsayin mu na ‘yan kasa, dole mu taka tamu rawar.”

Mr. Onanuga ya amince cewa abubuwa ba sa tafiya yadda shugaban kasa Bola Tinubu ke so a halin da ake ciki, Duk da haka, ya tabbatar da cewa a cikin watanni 12 masu zuwa, ‘yan Najeriya za su fara ganin sakamakon kokarin da gwamnatin ke yi don amfanin kasar.

“Kodayake mutane na korafi game da wahala, na fadawa BBC cewa matsalar tsadar rayuwa ta bazu a duniya baki daya. “Watakila abin da ke faruwa a duniya yanzu wani juyin zamani ne, kuma kasashe dole su shiga wasu wahalhalun.

“Muna cikin wannan yanayi, amma wannan gwamnati na yin kokari matuka wajen rage wahalhalun da jama’armu ke fuskanta.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply