Uwar gidan gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Isma El-Rufai ta ro?i mai gidanta da ya na?a mace domin maye gurbin Sarkin Zazzau, wanda ya rasu a ranar Lahadi.
A wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Twitter, ta ce domin tabbatar da daidaito tsakanin maza da mata, ta ro?i gwamnan kan cewa ko akwai yiwuwar a sake samun wata sarauniya a Masarautar Ta Zazzau kamar irin Sarauniya Amina?
Sai dai gwamnan bai amsa mata ba tukun kan wannan batu a halin yanzu, inda ko a jiya gwamnan ya ce ya du?ufa kan karanta littafin da wani Bature ya rubuta domin taimaka masa wajen yanke shawarar za?en sabon Sarkin Zazzau.
Har ya zuwa yanzu dai ana cigaba da dakon masu za?en sarki su mi?a sunayen masu neman sarautar Zazzau din ga mai girma Gwamnan jihar Kaduna, domin za?en wanda ya fi cancanta.
Sarautar Zazzau dai a ?ar?ashin Daular Fulani na da gidaje guda biyar ne, da suka ha?a da gidan Mallawa, da Katsinawa, sai Barebari da Sullubawa.