Mace Ya Kamata Ta Gaji Buhari A 2023 – Zainab Marwa

An bayyana cewa a bisa ga tsari da adalci mace ya kamata ta gaji mai girma Shugaban Kasa Buhari a shekarar za?e ta 2023 dake tafe domin samun daidaito da cigaba a ?asa.

Shugaba kuma wadda ta assasa kungiyar mata ta Aspire, Barista Zainab Marwa-Abubakar, ta bayyana hakan a ganawar ta da manema labarai a Abuja, inda ta ?ara da cewar akwai yiwuwar mace ta gaji Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar za?e ta 2023 dake tafe.

Ta fadi haka ne a ranar Lahadi a taron masu ruwa da tsaki na mata a Abuja. Shirin na daga cikin ayyukan bikin ranar mata ta duniya ta bana.

“Yayin da 2023 ke gabatowa, na yi imanin cewa mata za su ?auki ha??insu, a matsayinsu na shugabanni, masu tsara manufofi da masu yanke shawara a cikin wannan rawar neman mulki.

“A yanzu haka, ba mu gama haduwa ba har yanzu don zabar matar da za ta gaji Mai Girma, Shugaba Muhammadu Buhari. “Amma, me zai hana? Komai na iya faruwa, komai na iya yiwuwa, amma da lokaci mai zuwa,”.

“Ku (mata) dole ne ku ilimantar da kanku, musamman saboda kasancewar duk siyasa ta gari ce. “Don haka, dole ne ku je yankinku, ku ha?a kanku da ?ungiyar siyasa, siyasa ta, jam’iyyata, APC yanzu haka, tana rajistarta na jam’iyya da sake jaddadata a kewayen Najeriya.

Don haka, lallai ne ku je ku yi rijista da jam’iyyar siyasa sannan ku fara tsarawa, koya da kuma aikatawa.”

A nata bangaren, Kodinetan kungiyar ta kasa, Gift Johnbull, ta ce gina kasa wani aiki ne na hadin gwiwa kuma a zahiri matasa sune mahimman sinadari a gina ?asa, saboda haka ake bu?atar matasa su shiga siyasa. Ta ce ya kamata mata su yi imani da kansu kuma su san cewa su muhimman abubuwa ne wajen gina kasa.

Related posts

Leave a Comment