LOKACI YAYI DA GWAMNATIN JAHAR JIGAWA ZATA DAUKI NAUYIN MATSALAR CIWON KODA RANKATAKAF
……………………….
Ahmed Ilallah
A wannan lokaci bisa duba da irn talauchi da wahalar rayuwar da mutane suke ciki, ya zama dole Gwamnatin Jahar Jigawa, karkashin jagorancin Malam Umar Namadi, ta dauki nauyin masu fama da ciwan Koda dari bisa dari.
Kamar yadda a ka sani, jahar Jigawa musamman ma Jigawa ta Gabas sune kan gaba a wajen fama da matsalar ciwan Koda, ba ma a jahar nan ba, harma a kasa baki daya.
Ciwan Koda ya sanaddiyar rayukan dubban mutane a wannan jaha, kusan har yanzu ma tana ci gaba da kashe mutane.
Ciwan Koda ya talauta iyalai da yawa domin nemawa yan uwan su magani, kuma tana ci gaba da talauta iyalan da ibti’lain ya shafa.
Wannan na faruwa ne saboda rashin daukan nauyin wannan jinya dari bisa dari da hukumomi basu yi ba, musamman ita Jahar Jigawa.
A jigawa kusan za a iya cewa babbar asibitin kwanciya ta Hadejia ce take da bangare Wankin Kodar. Amma gudanar da wannan wuri kullum yana fuskantar kalubale kala kala, wani lokacin ma baya aiki, walau saboda lalacewar injin, ko rashin kayan aiki, wanda duka hali ne na ko in kula daga hukumomi.
Abin takaicin ma, a asibitin nan babu kwararran likita na dundundun a kan ciwukan da suka shafi koda.
Na biyu, hatta gudanar da aikin a wannan bangare kama-kama ce da wasu bayin Allah da suke bada gudunmawa.don ceton rayukan al’ummah, kai a takaice gudun mawar gwamnati bai wuci samar da ma’aikatan da suke wurin ba.
Duk da cewa jahar Jigawa na fama da matsaloli na kiwan lafiya daban daban. Amma fa matsalar Viwan Koda, wannan ba karamar annoba bace da take kashe mana al’ummah a kusan kowace rana.
Inda gwamnatocin a baya sun bada muhimmanci a kan wannan matsalar, da anjima da yin kandagarkin kamuwa da wannan ciwan, ta hanyar samar da ingantattun hanyoyin rigakafin wannan mummunar cuta.
Duk da cewa a Majalissar Tarayya ta Tara, tsohon Senator mai wakiltar Jigawa ta Gabas, Senator Ibrahim Hadejia ya gabatar da kudurin samar da Hukuma a kan Ciwan Koda a Jigawa, amma har yanzu ba a kai ga yin wannan wuri ba.
Ya kamata kamar yadda gwamnati jaha take daukan nauyin magani da rigakafin wasu chutukan, ita ma wannan matsalar kama yayi a bata kulawa ta musamman.
Ya kuma zama dole wakilan mu a Majalisar Kasa ta goma da suyi duk abu mai iyuwa don tabbatar da cewa wannan gwamnati ta samar da wannan cibiyar ma bincike akan ciwan koda da dangogin su.
alhajilallah@gmail.com (+23480 2595 1609)