Likitoci 53 Sun Harbu Da CORONA A Kano

Kungiyar Likitoci ta Nijeriya reshen jihar Kano ta ce ya zuwa yanzu ta rasa Likitoci 3 sakamakon cutar Covid-19 yayin da 53 suka harbu da cutar a cikin jihar.

Shugaban kungiyar reshen jihar ta Kano Usman Ali ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a ranar Litinin a garin Kano.

β€œHar yanzu muna tattara alkalumma ne bayan an samu wasu daga cikin Likitocin dauke da wannan cutar a cikin satin nan, wanda ya kai adadin kididdigarsu zuwa 53” a cewarsa.

Za’a iya cewa a dawowar cutar CORONA a karo na biyu cikin Najeriya abubuwa sun kara dagulewa fiye da farkon lokaci, inda adadin waΙ—anda suke kamuwa da cutar ke Ζ™ara hauhawa a kusan kullum.

A kwanakin baya shugaban kwamitin yaki da cutar na fadar Shugaban Kasa kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya zargi malaman addinai da yin kafar ungulu a shirin gwamnati na kawar da cutar, inda suka ci-gaba da buΙ—e wuraren ibadu masallata da coci-coci ba tare da bin ka’idojin kariya daga cutar ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply