Legas: ‘Yan Sanda Sun Damke Masu Zanga-zangar Farashin Mai

‘Ya’yan jam’iyyar SPN tare da hadin gwiwar matasa a jihar Legas sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da karin farashin mai da na wutar lantarki. Sai dai jami’an ‘yan sanda sun tarwatsa gungun masu zanga-zangar tare da kama wasu daga cikin jagororin zanga-zangar.

An kama masu zanga-zangar ne a yau, Alhamis, a yankin Ojuelegba da ke garin Legas. Bayan masu zanga-zangar da aka kama, an kwace kayan aikin wasu ‘yan jaridu.

Daya daga cikin jagororin masu zanga-zangar, Hassan Soweto, ya ce an kama mutum 18 da suka hada da ‘yan jarida.

“An kama mu tare da ‘yan jarida da ‘yan jam’iyyar SPN da safiyar yau (Alhamis) yayin da muka fito zanga-zangar nuna rashin amincewa da karin farashin man fetur da kudin wutar lantarki.” inji Soweto

Labarai Makamanta