Legas: Shugabannin Arewa Sun Bukaci DSS Ta Yi Gaggawar Sakin Sarkin Hausawa

Majalisar Shugabannin Arewa shiyyar jihar Legas sun yi kira da babbar murya ga hukumar DSS ta yi gaggawar sakin Sarkin Hausawan Legas Alhaji Aminu Idris Yaro da matarsa da suka kama ba tare da ɓata lokaci ba.

A cikin wata takardar sanarwa da majalisar ta fitar wadda ta samu sanya hannun sakataren ta Jarman Legas Alhaji Yerima Shettima, ta bayyana cewar Sarkin Hausawan na tsare a hannun DSS tun kwanaki uku da suka gabata ba tare da wata kwakkwarar hujja ba.

“Majalisar Shugabannin Arewa ta fahimci cewa kamun da aka yi wa Sarkin Hausawan na da jiɓi da wani bincike da hukumar ke yi akan dakataccen Gwamnan Banki Emefiele”.

Majalisar ba ta da wani sani akan dangantakar dake tsakanin Sarkin Hausawan da tsohon Gwamnan Bankin kamar yadda aka sani Emefiele na hulda da jama’a da dama a ciki da wajen Najeriya.

“Babban abin damuwar mu shine yadda Hukumar ta DSS ta kama Sarkin ba tare da wani bayanin dalilin kamun ba, wanda a fahimtar mu wannan wani shiri ne da ake dashi na taɓa mutuncin shugabannin mu na Arewa.

“Majalisar Shugabannin Arewa ba ta suka ko inkarin hukumar DSS ko wata hukuma ta tsaro ta gayyaci ko waye idan bincike ya biyo ta kanshi, sai dai abin da muke cewa akan kama Sarkin Hausawa da aka yi shine an tsare shi sama da awannin 24 wanda hakan ya saɓa dokar ƙasa da ba za a amince dashi ba”.

“Majalisar Shugabannin Arewa da kafatanin ‘yan arewa dake zaune a kudanci suna girmamawa gami da martaba Sarkin Hausawan kasancewar shi dattijo mai mutunci da kamala a tsakanin jama’a ƙasa baki daya.

“Bisa ga haka majalisar shugabannin Arewa na ƙara yin kira ga DSS da dukkanin wata hukuma da abin ya shafa da a yi gaggawar sakin Sarkin Hausawan ba tare da wani sharaɗi ko ɓata lokaci ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply