Layya: Sarkin Musulmi Ya Jagoranci Rabon Miliyan 17 Ga Mabuƙata

A ranar Talata 28/7/2020 mai Alfarma Sarkin Musulmi, kuma Shugaban majalisar koli kan Harkokin Addinin Musulunci a Nijeriya, Alh. Muhammad Sa’ad Abubakar ya jagoranci raba kudin sayen shanu na shekara-shekara da gwamnatin jihar Sokoto ke yi. An yi taron ne a fadar Sarkin Musulmi dake Sakkwato.

A jawabin da ya gabatar, Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya yi kari ga iyayen kasar da su ji tsoron Allah su sani wannan amana ce dan haka su yi abin da ya ce, kuma ba za su lamunce wa duk wanda ya yi ba daidai ba. Ya kuma bada umurnin cewa kowace gunduma su dinga zama suna tattanawa akan yadda aka gudanar da ayukkan su, kana su da kawo rahoton zuwa 29 ga watan Muharram.

Sarkin Musulmi ya kuma yabawa gwamnatin jihar Sokoto akan wannan kokarin, ya kuma yabawa Hukumar zakka da wakafi ta jihar Sokoto akan kokarin da suke yi na kwatantawa akan amanar da aka ba su.

A nasa jawabin, Shugaban zartarwar hukumar Malam Muhammad Lawal Maidoki Sadaukin Sakkwato ya bayyana cewa a wannan shakarar Gwamnan jihar sokoto Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya aminta da kashe naira milyan goma sha bakwai da dubu dari biyu (17,200,000:00) domin rabawa iyayen kasa 86 da ke cikin kananin hukumomin jihar 23, domin sayawa marayu,tsoffi da mabukata shanun layya, kamar yadda aka saba duk shekara, inda ya bayyana cewa a wannan shekarar kowace gundumar za a bata naira dubu dari biyu domin sayawa marayu, mabukata da tsoffin dake gundumomin, maimakon naira dubu dari da saba’in (170,000:00) da aka bada a bara, lura da tashin kudin dabbobin.

Shugaban ya bayyana cewa makasudin yin layyar shine, domin a farantawa yara marayu rsi kuma a sanya masu farin ciki kamar sauran masu iyaye.

Sadaukin Sakkwato, ya kuma bada rahoton layyar shekarar bara, ya kuma gabatar da wasu sabbin shirye-shirye da hukumar ke sa ran aiwatarwa bada jimawa ba na taimakon al’umma a bangarorin wakafin itatuwa a fannin Ilimi, wakafin itatuwa ga sabbin aure, wakafin harkar noma na wani mutum Mr. Jack da sauransu.

An zabi gundumar Dangi Shuni ta zama inda za a yi taron kaddamar da dashen itacen wakafi na wannan shekarar. Ya bayyana hubbasar wasu gundumomin da suke kara kudi bisa ga abin da ake ba su.

Taron ya samu halartar Wazirin Sokoto Farfesa Sambo Junaidu, Galadiman Gari, Sarkin Yakin Binji, Ardon Shuni, da sauran wasu ‘yan Majalisar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Daukacin Iyayen kasa, Sabon mukaddasin Daraktan Zakka kuma daraktan tsare-tsare na hukumar, Malam Murtala Garba Alkali, Mukaddasin Daraktan Kudi da na Wakafi da sauran ma’aikatan Hukumar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply