Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Lantarki: ‘Yan Najeriya Zasu Dara Kwanan Nan – Ministan Lantarki

Ministan wutar lantarki Saleh Mamman ya ce nan ba da dadewa ba, ‘yan Najeriya zasu yi alfahari da yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gyara fannin wuta.

A ranar Laraba, ministan ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda yace, wannan mulkin ya samar da cigaba mai tarin yawa a ma’aikatar wutar lantarki.

Mamman ya ce wannan mulkin a shirye yake da yayi gyara a bangarorin da ya lalace.

“Nan ba da dadewa ba, ‘yan Najeriya zasu waiwaya baya cikin alfahari, su ce lallai mulkin Shugaba Buhari yayi gyara mai tarin yawa a fannin wutar lantarki.

“Yanzu haka mun samu cigaba sosai, kuma muna sanar da ‘yan Najeriya abinda ake ciki.”

A shekarar 2019, shugaban kasa yasa hannu akan wata yarjejeniya ta wutar lantarki da Siemens AG, wani kamfani dake kasar Jamus, wadanda zasu dinga bayar da megawatts 7000 na wuta a shekarar 2021.

A watan Mayu, Buhari ya aminta da bada kudi a kashi na farko don yarjejeniyar wutar lantarkin Siemens.

Exit mobile version