Lallai A Kama Aisha Buhari Sakamakon Cin Zarafin Dalibin Da Ta Yi – Naja’atu Mohammed


A hira da gogaggiyar ƴar siyasa kuma mai kare hakkin ɗan Adam, Naja’atu Mohammed ta yi kira ga rundunar tsaron Najeriya su gaggauta yin awon gaba da uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari, saboda kama wani Aminu Mohammed da tasa aka yi sannan ta rika jibgarsa.

Idan ba a manta ba Aisha Buhar ta sa an tattaki tun daga Abuja zuwa garin Dutse inda aka kama wani matashin ɗaliɓi wai don ya saka rubutu da ya shafi uwargidan a shafin tiwita.

Jaridar Daily Nigerian ta buga hira da ta yi da Naja’atu in da ta nuna bacin ranta da yin kira ga uwargidan shugaban kasa da kakkausar murya cewa ta gaggauta sakin wannan matashi sannan kuma rundunar tsaron kasa su kamata su tsare ta

” Ya ya za a ce wai irin waɗannan matasa da suka zaɓi mijin ki shugaban kasa kuma ace wai za arika yi musu da sauran jama’a mulkin kama karya. Ba za ta saɓu ba.

” Nan kika fito kika rika ƙorafun Mamman Daura ya yi kaza ya yi kaza, me aka yi, amma ki ba za ace miki gashi ba, sai kawai kiyi amfani da karfin gwamnati ki rika taka mutane. Ba za sa ido mu bari kina abinda kika dama ba.

Naja’atu ta ce wannan ba shine na farko ba, kin taba sa wa an daure wani hadiminki da kika yi mishi zargin wafce miki da naira biliyan 2, haka kuma wata hadimar ki itama. Kawai kina ta yin abu ba a iya ce miki komai. Sannan kuma ke kina da baki ba a iya ce miki komai.

” Ƴan Najeriya Buhari suka zaɓa ba ke ba, saboda haka karya doka ne ki rika amfani da karfin kujerar sa kina karya doka kina ciwa mutane mutunci yadda kika so.

Idan ba don irin shugaba Buhari da ya bar wawukeken giɓi ba a gwamnatin sa, kowa kawai sai ya karkace ya rika yin abinda ya ga dama bau mai ce masa ƙala.

Labarai Makamanta

Leave a Reply