Kwastam Ta Kama Fetur Na Miliyoyi Ana Yunkurin Fitarwa Waje

Hukumar Kwastam da ke ya?i da fasa kwabri ta ?asa ta ce ta kama man fetur da ya kai kimanin lita 81,425 da ake shirin fita da shi daga ?asar.

Hukumar ta ce ta kama man fetur ?in a Badagry da ke Legas da kuma kan iyakar Najeriya da Jamhuriyyar Benin.

A wani sa?o da hukumar ta kwastam ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce an ?ura man fetur ?in cikin duro-duro kusan 60 sa’annan aka saka wani man a cikin buhuna da ku ma jarkoki.

Hukumar ta ce darajar man fetur ?in da jami’anta suka kama ya kai sama naira miliyan 13.

Related posts

Leave a Comment