Kwankwaso Ya Shawarci Matasa Da Shiga Jam’iyyar NNPP

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso, ya bukaci ‘yan Najeriya musamman matasa da su shiga jam’iyyar NNPP don dawo da Najeriya da samar da rayuwa mai kyau da ‘yan kasa ke so.

Kwankwaso wanda ya yi wannan kiran yayin babban taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar a Abuja, ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP ta shirya fwajen ceto al’ummar kasar.

A cewar tsohon gwamnan, sabuwar jam’iyyar za ta tabbatar da ayyukan yi, da ingantaccen ilimi ba tare da yajin aikin ba, da dai sauransu ga matasan kasar nan.

Ya kuma bukaci matasa da su yi rajista da jam’iyyar da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) domin su karbi katin zabe su zabi jam’iyyar a 2023.

“NNPP iska mai kyau ce ga ‘yan Najeriya saboda ‘yan kasar suna neman sabuwar Najeriya ne kuma mafi inganci tun da sun gaji da halin da ake ciki.” Kwankwaso ya ce idan har aka yi haka, duk kalubalen da ake fuskanta a yanzu za a manta da shi idan NNPP ta samu mulki.

Ya kara da cewa: “Wannan jam’iyyar ta dukufa wajen gyara kurakuran da aka yi a baya kuma da goyon bayanku za mu samu ingantacciyar Najeriya.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply