Ministan Neja-Delta, Godswill Akpabio ya shaida wa kwamitin majalisa ranar Litini cewa mafi yawan kwangilolin da hukumar NDDC ke ba da wa, ‘yan majalisar Kasa ake rarrabawa.
Wannan kalamai na Akpabio ya harzuka ‘yan kwamitin dake sauraren sa a lokacin da yake jawabin sa.
Dakin taro dai ya barke da hayaniya kafin daga baya komai ya lafa.
Kusan duka shugabannin sassan hukumar sun bayyana yadda aka rika kashe mu raba a tsakanin manyan darektocin hukumar da kuma ma’aikata.
Manajan Darektan riko na hukumar raya yankin Neja-Delta, Kemebradikumo Pondei, ya bayyana cewa kazafi da sharri aka yi musu cewa da kayi wai sun kasafta naira bilyan 1.5 a tsakanin su matsayin tallafin Korona, ” Mu naira 1.3 muka kasafta”.
Pondei ya fadi haka ne da yake amsa tambayoyin ‘yan majalisa a majlisar tarayya ranar Litini.
Idan ba a manta ba a zaman farko na kwamitin, sai da Pondei ya rika suma har aka garzaya da shi Asibiti
” Wannan kudade mun raba wa matasa, mata, miskinai, da wadanda basu da galihu a matsayin tallafi.
Yadda Hukumar NDDC ta kasafta a tsakaninta dumbuzum kudade wai na tallafin Korona
Manajan Daraktan Riko na Hukumar Bunkasa Yankin Neja Delta (NDDC), Kemebradikumo Pondei, ya yi ikirari da bakin sa cewa hukumar ta yi wa naira bilyan 1.5 rabon-tuwon-gayya a tsakanin ma’aikatan ta, a matsayin tallafa musu lokacin zaman gida dole saboda Coronavirus.
Ya yi wannan furucin ne a lokacin zaman binciken yadda wata naira bilyan 40 ta yi fukafuki, kuma har yau aka rasa kan bishiyar da kudin suka dira.
Kwamitin Majalisar Dattawa da aka nada na mutum bakwai tun a ranar 5 Ga Mayu, shi ne aka dora wa nauyin binciken “yadda aka ragargaji kudade” a zargin da ake yi wa sabbin shugabannin rikon NDDC.
Majalisar Dattawa ta ce a cikin watanni uku, NDDC ta kashe naira bilyan 40 ba bisa ka’ida ba. Wannan kuwa kara haifar da zargi kan Hukumar daga bangaren masu hakki a karkashin ta.
“An kuma zargi Shugabannin Rikon NDDC da laifin yi wa ma’aikatan hukumar kwasar-karan-karan mahaukaciya, su na watsar wa a waje, ba bisa ka’idar korar ma’aikata daga aiki ba.”