Kwangilar Gas: Najeriya Ta Yi Nasara Akan Kamfanin Birtaniya

Gwamnatin Najeriya ta samu nasarar karin wa’adin lokaci don daukaka kara gaban kotu a shari’ar da ta ke da katafaren kamfanin Birtaniya na P&ID kan kwangilar gas da kamfanin ke zargin kasar da saba ka’idoji.

Nasarar da Najeriya ta samu a jiya juma’a gaban kotun Birtaniyar, na nuna cewa ta na da cikakkiyar damar kalubalantar hukuncin watan Agustan bara da ya yi umarnin kwace mata kadarorin da yakai darajar dala biliyan 9 da miliyan 600 da ke matsayin kashi 1 bisa 5 na yawan kudadenta da ke asusun ketare.

Cikin watan Satumban bara ne gwamnatin Najeriyar ta daukaka kara duk da cewa ta saba wa’adin da aka dibar mata don daukaka karar wanda shima ya haddasa mata asarar akalla dala miliyan 200.

A hukuncin kotun kasuwancin na yau Juma’a karkashin jagorancin mai shari’a Ross Cranston ya bai wa Najeriyar karin lokaci don shiryawa tare da gabatar da kwararan hujjojin da za su kalubalancin hukuncin farko.

Najeriyar dai na fuskantar tuhuma ne kan kin mutunta yarjejeniyar kwangilar aikin gas da za a yi amfani da shi wajen samar da lantarki tsakaninta da kamfanin na P&ID tun cikin shekarar 2010.

Umar Jibrilu Gwandu shi ne mai magana da yawun babban mai shigar da kara kuma ministan shari’ar Najeriyar ya ce kasar na da hujjojin da ke nuna tun farkon kafuwar yarjejeniyar an yita ne bisa cuta.

Tun bayan hawan mulkin shugaba Muhammadu Buhari a 2015 ne ya bukaci bincikar batun kwangilar wadda aka yi imanin ta na cike da cuwa-cuwa daga bangarorin biyu, yayinda a 2017 Najeriyar ta sanar da kama wasu ‘yan Birtaniya biyu da laifin cuta baya ga badakalar kudi da ke da alaka da kwangilar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply