Gwamnatin tarayya ta tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa nan ba da dadewa ba za a fara sayar da man fetur a farashi mai matukar sauki, wanda jama’a za su dara.
Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana hakan a karamar hukumar Egbema da ke jihar Imo yayin rangadin da ya je karamar matatar man fetur da za a kaddamar a wata mai zuwa.
Da irin wannan matatun, ministan ya ce dukkan magana a kan tallafin man fetur zai zama maras amfani saboda za a dinga samunsa a farashi kalilan.
Ya bayyana kafa kananan matatun man fetur din a kasar a matsayin wata hanya da za a samu sauki a wannan mulkin na shugaba Buhari.
“Za mu iya bayyanawa ‘yan Najeriya cewa, kusan kowacce gwamnati a Najerya ta dinga magana a kan kananan matatun man fetur. Babu gwamnatin da za ta ki aminta da wannan lamari domin cigaba”