Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Kwamitin Wanzar Da Zaman Lafiya Ya Kalubalanci ‘Yan Takarar Shugabancin Kasa

Kwamitin wanzar da zaman lafiya ?ar?ashin jagorancin tsohon shugaban ?asa Abdulsalam Abubakar, ya yi kira ga ?an takarar shugabancin ?asar da su mayar da hankali wurin ganin an gudanar da za?e lami lafiya ba tare da wani rikici ba.

Kwamitin ya nuna rashin jin da?insa kan yadda ake samun ?aruwar rikice-rikice a wuraren gangamin ya?in neman za?e a fa?in ?asar.

Kwamitin, wanda aka kafa domin tabbatar da an yi zabe cikin zaman lafiya da lumana wato NPC ya bayyana cewa akwai matsaloli da ke barazana ga za?en da ke tafe, hakan ne ya sa kwamitin ya bukaci a yi wa tufkar hanci.

Kwamitin ?ar?ashin jagorancin tsohon shugaban kasar Abdulsamai Abubakar ya yi kira ga ?an takarar shugabancin ?asar a duka jam’iyyu da su ja kunnen masu magana da yawunsu da magoya bayansu da tabbatar da cewa sun yi iya bakinsu domin gudun tayar da zaune tsaye a lokacin yakin neman zabe da kuma lokacin zaben kansa.

Ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake amfani da munanan kalaman da ba a taunawa da barazana da kuma yadda ake samun arangama tsakanin magoya bayan jam’iyyu.

Haka kuma ya ce ?an Najeriya sun damu matu?a kan yadda wasu ?an siyasa suke wasu abubuwan da ba su dace ba a cikin ?an kwanakin nan.

Haka kuma kwamitin ya ce idan ba a shawo kan wadannan matsalolin ba, za su iya kawo cikas ko kuma tasgaro ga yarjejeniyar zaman lafiyar da duka ?an takarar shugabancin kasar suka ratta?a wa hannu a watan Satumba.

Wannan kiran da kwamitin ya yi na zuwa ne bayan shugaban hukumar zaben Najeriya Mahmood Yakubu ya zargi ?an siyasa da cewa suna ?ara zafafa fagen siyasa da kuma rashin bin dokoki.

Haka kuma ?asashen Birtaniya da Amurka sun nuna damuwa kan yadda ake ?ara zafafa hare-hare kan ofisoshi da kayayyakin hukumar za?en Najeriya inda suka ce duka wa?annan za su iya kawo tasgaro ko na?asu ga za?en 2023.

Ko a makon da ya gabata sai da wasu da ake zargin ?ata gari ne suka ?ona ofisoshin na Inec a jihohin Ogun da Osun.

KINEC din ta ce tsakanin Fabrairun 2019 zuwa Mayun 2021, an kai hare-hare kan ofisoshinta da kayayyakinta sau 41 a jihohi 14 na kasar.

Exit mobile version