Kwamitin Wanzar Da Zaman Lafiya Ya Kalubalanci ‘Yan Takarar Shugabancin Kasa

Kwamitin wanzar da zaman lafiya ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban ƙasa Abdulsalam Abubakar, ya yi kira ga ƴan takarar shugabancin ƙasar da su mayar da hankali wurin ganin an gudanar da zaɓe lami lafiya ba tare da wani rikici ba.

Kwamitin ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda ake samun ƙaruwar rikice-rikice a wuraren gangamin yaƙin neman zaɓe a faɗin ƙasar.

Kwamitin, wanda aka kafa domin tabbatar da an yi zabe cikin zaman lafiya da lumana wato NPC ya bayyana cewa akwai matsaloli da ke barazana ga zaɓen da ke tafe, hakan ne ya sa kwamitin ya bukaci a yi wa tufkar hanci.

Kwamitin ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban kasar Abdulsamai Abubakar ya yi kira ga ƴan takarar shugabancin ƙasar a duka jam’iyyu da su ja kunnen masu magana da yawunsu da magoya bayansu da tabbatar da cewa sun yi iya bakinsu domin gudun tayar da zaune tsaye a lokacin yakin neman zabe da kuma lokacin zaben kansa.

Ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake amfani da munanan kalaman da ba a taunawa da barazana da kuma yadda ake samun arangama tsakanin magoya bayan jam’iyyu.

Haka kuma ya ce ƴan Najeriya sun damu matuƙa kan yadda wasu ƴan siyasa suke wasu abubuwan da ba su dace ba a cikin ƴan kwanakin nan.

Haka kuma kwamitin ya ce idan ba a shawo kan wadannan matsalolin ba, za su iya kawo cikas ko kuma tasgaro ga yarjejeniyar zaman lafiyar da duka ƴan takarar shugabancin kasar suka rattaɓa wa hannu a watan Satumba.

Wannan kiran da kwamitin ya yi na zuwa ne bayan shugaban hukumar zaben Najeriya Mahmood Yakubu ya zargi ƴan siyasa da cewa suna ƙara zafafa fagen siyasa da kuma rashin bin dokoki.

Haka kuma ƙasashen Birtaniya da Amurka sun nuna damuwa kan yadda ake ƙara zafafa hare-hare kan ofisoshi da kayayyakin hukumar zaɓen Najeriya inda suka ce duka waɗannan za su iya kawo tasgaro ko naƙasu ga zaɓen 2023.

Ko a makon da ya gabata sai da wasu da ake zargin ɓata gari ne suka ƙona ofisoshin na Inec a jihohin Ogun da Osun.

KINEC din ta ce tsakanin Fabrairun 2019 zuwa Mayun 2021, an kai hare-hare kan ofisoshinta da kayayyakinta sau 41 a jihohi 14 na kasar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply