Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Bauchi Ya Nemi Haɗin Kan Jama’a

Sabon Kwamishinan yan’sanda na Jihar Bauchi, Sylvester Abiodun Alabi, ya kama aiki tare da neman hadinkan al’umman Jihar da su taimaka masa ta wajen bankado masu aikata miyagun laifuka, da kuma dakile yan tada zaune tsaye, tare da masu sace-sace da kwacen kayan mutane a cikin gari.

Kwamishinan yace babban muhimmin abu a hidimar tsaro shine dole sai anyi amfani da hikima ta wajen zamanan tar da yadda za su rika tunkarar matsalolin da Jami’an tsaro ke fuskanta, a yun’kurinsu na tsare lafiya da dukiyan al’umma.

Yace manufofin su na jami’an tsaro shine jagoran gudanar da aikinsu na tabbatar da bin doka da oda ga ko wani dan Najeriya, a ko ina yake da kuma bada fifiko kan kyautata rayuwar dan-adam tare da bincike mai inganci.

Alabi ya kara da cewa lallai dole ne hidimar tsaro sai mutanen gari sun shigo ciki domin a hada hannu tare, saboda muhimmanci samun bayanai ba tare da shakkan kowa ba, komai mukami da yake dashi a cikin al’umma, duk wanda yayi shima za’ayi masa!

Sa’ annan yace zasu hada duk wata alaka da sauran Jami’an tsaro a Jihar domin samun nasarar aikinsu, da Kuma yin amfani da kayan aiki na zamani.

Daga karshe kwamishinan yace dole.ne Jami’an yan’sanda susan matsayin su da kuma samun hadinkan a kan aikinsu, da abin da yakamata su sani a lokacin gudanar da sintiri a fadin Jihar baki daya

Daga Adamu Shehu Bauchi

Labarai Makamanta

Leave a Reply