Kwalara: Gwamnatin Tarayya Ta Shawarci ‘Yan Najeriya Su Kaurace Wa Shan Fura, Kunu Da Zobo

images (92)

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa dngane da yaduwar cutar kwalara, gwamnatin tarayya ta bukaci ƴan Najeriya da su guji shan abin sha na gida irin su kunu, zobo da fura domin gujewa ɓarkewar cutar kwalara.

Karamin Ministan Muhalli, Iziaq Salako ne ya bayar da shawarar a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, a ranar Litinin.

Salako ya hori ƴan Najeriya da su ɗauki matakan kariya kamar tsaftace muhallinsu a koda yaushe da zubar da shara yadda ya kamata a wuraren da aka kebe.

Labarai Makamanta

Leave a Reply