Kwa?ayi Ya Sa ‘Yan Najeriya Satar Tallafin CORONA Ba Yunwa Ba – Fadar Shugaban Kasa

An bayyana cewar satar da wasu ?ata garin ‘yan Najeriya suka rin?a yi na fasa Rumbunan kayayyakin tallafin CORONA da sauran shagunan bayin Allah, ko ka?an bai ala?a da batun yunwa ko talauci, tsabar kwa?ayi ne kawai da son zuciya.

Mai magana da yawun Shugaban ?asa Mista Femi Adesina ya bayyana hakan a hirar da yayi a shirin Sunrise Daily na tashar Channels TV ya ce malalata da batagari ne kawai sukayi amfani da zanga-zanga wajen satan kayan abinci.

Ya ce sam bai amince da bayanan da wasu ke yi ba cewa yunwa ta sa mutane ke wawusan kayan abinci ba.
“Ban yarda da maganar nan (cewa masu wawusa yunwa suke ji ba) saboda laifi laifi ne, ta yaya zata halatta sata saboda kawai mutum na jin yunwa”.
“Kamar yadda ba zaka halatta fashi da makami don mutum na fama da talauci ba, ba zaka iya halatta sace-sacen da ake yi yanzu ba. Wannan Son zuciya ne zalla.”

“Ba dukkan wadanda ke wawusan ke jin yunwa ba, maganar gaskiya kenan. Zallan kwadayi ne kawai da laifi. Ya kara da cewa halin da kasar ke ciki ta haifar da rikici a ko’ina kuma ta bada daman sace-sace da fashe-fashe.

Related posts

Leave a Comment