Kuskure Ne Matakin Gwamnati Na Kai Tubabbun Boko Haram Waje Karatu – Indabawa

Matakin daukan nauyin karatun tubabbun ‘yan Boko Haram a kasashen waje da gwamnatin Buhari ke kokarin zartarwa kuskure ne, idan har gwamnati ba za ta dauki nauyin marayun da ‘yan ta’adda suka kashewa iyaye ba, bai kamata su ‘yan ta’addan su sami wannan gata ba.

Dama manazarta sun bayyana cewa kuskure ne sakin tubabbun ‘yan ta’adda da gwamnati ke yi, kusan karo uku kenan da aka sami labarin aika-aika wasu daga wadannan sakakkun ‘yan ta’adda, inda a ciki har akwai wanda ya kashe mahaifinsa ya kora shanunsa.

Mu dai bamu san abin da gwamnatin Buhari ke nufi da mu ba ‘yan arewa, kullum kashe mu ake ko a jikinsa, ya kulle mana bodoji abinci ya yi tsada komai ya lalace.

Kwana kadan jami’an anti-daba suka kashe mutane biyu a Kano unguwar Sharada bisa zalunci, kanzil bai ce ba, ko ban fada muku ba kun san idan da a Kudu ne dole ya fito ya yi jaje ya kuma bada tabbacin za a dauki mataki, amma da ke musulmai ne ‘yan Arewa ko a jikinsa.

ALLAH YA NA MADAKATA.

Related posts

Leave a Comment