Kuskure Ne Ba Qatar Damar Daukar Bakuncin Gasar Cin Kofin Duniya – Tsohon Shugaban FIFA

Tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA ya ce an yi kuskure da aka bai wa Qatar damar karɓar bakuncin gasar cin Kofin Duniya.

Sepp Blatter wanda ya shugabanci hukumar FIFA lokacin da aka ɗauki matakin a 2010, ya bayyana cewa an yi wa hukumar matsin lamba kuma da alama kuɗi ya yi tasiri wajen yanke shawarar.

Ana zargin Qatar da cin hanci da kuma cin zarafin ma’aikata a wuraren gine-gine.

An kuma soki ƙasar kan yadda take tafiyar da al’amuran masu ra’ayin auren jinsi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply