Kungiyoyin Kwadago Sun Gabatar Da ₦615,000 A Mafi Karancin Albashi

IMG 20240308 WA0067

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Ƙungiyoyin ƙwadago sun gabatar da mafi ƙarancin albashi da suke so gwamnati ta biya ma’aikata a duk ƙarshen wata.

Ƙungiyoyin na TUC da NLC sun cimma matsayar N615,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi da suke son ma’aikata su riƙa samu, wannan matsayar dai tuni suka sanar da gwamnati bayan sun kammala tattaunawa a tsakaninsu.

An ruwaito wani babba ne a ƙungiyar ƙwadago da ya nemi a sakaya sunansa shi ne ya tabbatar da cewa N615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin.

Majiyar wanda yana cikin kwamitocin da gwamnati ta kafa domin samar da sabon mafi ƙarancin albashin, ya ce kuɗin za su iya ƙaruwa biyo bayan ƙarin kuɗin wutar lantarki da aka yi.

“Mu a NLC da TUC mun miƙawa gwamnati abin da muke buƙata kan mafi ƙarancin albashi wanda shi ne N615,000. Wannan ita ce matsayar TUC da NLC kan batun. Mun sanar da gwamnati hakan.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply