Kungiyoyin Arewa Sun Yi Kiran A Janye Dakatarwar Da Aka Yi Wa Sanata Ningi

IMG 20240309 WA0082

Gamayyar kungiyoyin Arewa ƙarkashin wata kungiya mai suna RAID da aka kafa domin cigaban Arewacin Najeriya ta bukaci majalisar dattawa ta dawo da Abdul Ningi.

Kungiyar RAID tana Allah wadai da yadda aka dakatar da Sanatan Bauchi ta tsakiya daga majalisa tare da yin tir da abin da ‘yan majalisar suka yi.

Kungiyar tana ganin cewa an takawa ‘dan majalisar burki ne saboda ya yi namijin kokari wajen bankado irin rashin gaskiyar da ake tafkawa. RAID ta ce wannan mataki da aka dauka ya jawo an toshe bakin daya daga cikin manyan ‘yan siyasan da ke magana da yawun yankin Arewa.

Wannan matsaya ta fito daga bakin shugaban RAID, Balarabe Rufai a wani taron manema labarai da ya kira a Abuja a karshen makon nan.

“Yunkurin Sanata Ningi na haska rashin gaskiyar da aka lullube namijin kokari ne kuma abin da ake bukata.” “Sai dai korarsa daga zauren majalisar dattawa bala’i ne, mun rasa daya daga cikin masu magana da yawunmu.”

 

Labarai Makamanta

Leave a Reply