Kungiyar Matasan Arewa Ta Yi Tir Da Yunkurin Dakile Belin Abba Kyari

images (71)

Kungiyar cigaban Matasan yankin arewacin Najeriya AYCF ta yi tir gami da Allah wadai da yunkurin tauye ‘yanci da hakkin jajirtaccen ɗan Sanda Abba Kyari wanda a yanzu haka yake fuskantar shari’a a gaban kotu ta hanyar dakile bayar da belin sa.

A cikin wata takardar sanarwa da kungiyar ta fitar wadda ta samu sanya hannu shugabanta na ƙasa Yerima Shettima, Ƙungiyar ta bayyana cewar bayar da beli wani hakki ne da doka ta tanada a ba waɗanda ake zargi da laifi su samu damar walwala har zuwa lokacin da Kotu za ta yanke hukunci, idan wanda ake zargi ko tuhuma ya samu belin Kotun, zai taimaka masa wajen gudanar da harkokin su bisa ga tsarin doka.

Yerima Shettima ya ƙara da cewar babu tababa Abba Kyari ya samu beli bisa ga ka’ida da doka ta tanada, wanda babu wani dalili na cigaba da tsare shi bayan ‘yancin da ya samu.

Kungiyar ta Matasan ta jaddada kira akan muhimmancin martaba doka da oda ta hanyar ba jajirtaccen ɗan Sandan ‘yancin da doka ta bashi na beli ba tare da wani bata lokaci ba.

“Muna kira ga bangaren sharia da cewar martaba doka shi ne babban mataki na cimma nasara, saboda haka dukkanin wani yunkurin tauye hakkin Abba Kyari na hana shi ‘yancin da doka ta bashi zalunci ne karara wanda ba zai haifar da ɗa mai ido ba”

Labarai Makamanta

Leave a Reply