Kungiyar Mahaddata Kur’ani Sun Bukaci A Cire El-Rufai Daga Jerin Sunayen Ministoci

Gamayyar Mahaddata Al-Qur’ani sun yi kira ga Majalisar Dattawa da ta ki Amincewa da sunan Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai. Sunansa na cikin Ministoci 28 da Shugaban ?asa Bola Tinubu ya mika Domin tantancewa.

A yayin zantawa da manema labarai a Bauchi Yau Lahadi, Sheikh Sidi Ali, daraktan ilimi na Gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya roki Shugaba Tinubu da ya cire Sunan El-Rufai daga cikin jerin sunayen Ministocin sa.

Malamin ya bayar da hujjar cewa na?a El-Rufa’i a Matsayin Minista ya saba wa ka’idojin adalci, daidaito da kuma sanin yakamata. Ya kuma jaddada cewa, Domin tabbatar da adalci, zaman lafiya, Da kuma cigaban kasa, bai kamata a yi amfani da ire-iren su El-Rufai ba.

Sheikh Sidi Ali ya bayyana damuwarsa kan abubuwan da El-Rufa’i ya yi a baya, musamman game da yadda aka yi wa daliban Al-Qur’ani a lokacin da ya kore su daga gidan Maulana Sheikh Dahiru Bauchi da karfin tsiya ta hanyar amfani da hayaki mai sa hawaye, Inda ya nuna Rashin mutunta ‘yancinsu da ‘yancin Addininsu.

Gamayyar kungiyoyin sun yi kira ga shugaba Tinubu da ya cire sunan El-Rufai daga jerin sunayen da aka aika wa Majalisar Dokokin ?asar Domin samar da zaman lafiya, Da kwanciyar hankali da mutunta dokokin kasa. Ta yin hakan, sun yi imanin za a yi adalci ga al’ummar Al-Qur’ani da kuma dukkan ‘yan Nijeriya.

Related posts

Leave a Comment