Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar likitoci ta ƙasar ta yi kiran da a fara aiwatar da yin gwajin ƙwaƙwalwa ga ‘yan takarar siyasa domin samar da shugabanni nagari.
Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da kungiyar ta fitar kuma aka rarraba ga manema labarai a Abuja.
Sanarwar ta bayyana cewar kiran ya zamo wajibi ta la’akari da irin fara saƙa da mugun zare da mafiyawancin ‘yan siyasa ke aikatawa.
“Tabbas matukar an ɗauki wannan mataki za a yi nasara a kokarin da ake dashi na ganin an samu shugabannin da suka dace waɗanda za su yi kyakkyawar jagoranci domin kai ƙasar gaba”.
Sai dai wannan mataki na kungiyar likitocin ya haifar da surutai a ƙasar inda wasu ke ganin dacewar hakan yayin da wasu ke ganin akasi.