Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar kwadago (NLC) ta ce za ta ci gaba da yajin aikinta na dakatar da masana’antu da harkokin yau da kullum a jihar Kaduna.
Kungiyar ta umarci mambobinta na jihohi da su yi shirin ko ta kwana don amsa kira nan ba da jimawa ba.
Shugaban NLC, Kwamared Ayuba Wabba ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron gaggawa na Majalisar Zartarwar kungiyar ranar Talata a Abuja.
Wabba ya zargi gwamnan jihar Kadunan Nasir El – Rufai da kin mutunta yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnatin tarayya ta kulla tsakanin NLC da gwamnatin jihar.
Ya ce bayan taron da majalisar zartarwarsu ta yi, ta daddale cewa tun da ta bi duk hanyoyin da suka kamata ciki har da rubuta wasiku zuwa ga Shugaba Muhammadu Buhari da Ministan kwadago Chris Ngige amma bata sauya zani ba, kungiyar ta yanke shawarar sake komawa yajin aikin.