Kungiyar Kasuwanci: PDP Ta Yaba Buhari Kan Goyon Bayan Ngozi

Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta jinjinawa shugaba Muhammadu Buhari bisa goyon bayan da ya nunawa tsohuwar Ministar ku?i Dr Ngozi Okonjo Iweala a takaran da ta yi na shugabancin kungiyar kasuwancin duniya wato WTO.

Shugaban uwar jam’iyyar, Uche Secondus, yayi wannan jinjinawan a jawabin da mai magana da yawunsa, Mr Ike Abonyi, ya saki ranar Laraba a babban birnin tarayya na Abuja.

Secondus ya ce Najeriya ta kafa tarihi a zaben da aka yi wa Okonjo-Iweala matsayin mace ta farko a duniya da ta zama shugabar kungiyar kasuwanci ta WTO.

Ya yabawa shugaban Buhari kan ajiye siyasa gefe da yayi wajen goyawa Okonjo-Iweala baya da kuma Dr Akinwumi Adesina, shugaban bankin cigaban Afrika (AfDB) bayan da yayi har suka samu nasara.

Ya ce nasarar Okonjo Iweala na zuwa ne bayan tazarcen Adesina matsayin shugaban bankin AfDB, kuma hakan ya farantawa PDP rai saboda dukkan wadannan mutane biyu tsoffin Ministoci ne a gwamnatin PDP.

Mun kawo muku rahoton cewa Tsohuwar ministar kudin Najeriya, Dr Ngozi Okonjo Iweala zata zama sabuwar Dirakta Janar na kungiyar kasuwancin duniya.

A cewar majiyoyi daga gamayyar kasashen Turai, za ta zama shugabar kungiyar ne bayan nasara kan Yoo Myung-hee, yar kasar Koriya ta kudu, idan akayi zaben ranar 9 ga Nuwamba. Kasashe 27 da ke karkashin kungiyar Turai ta EU su na goyon bayan tsohuwar ministar tattalin Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweala a zaben WTO.

Related posts

Leave a Comment