Kungiyar Direbobin Sun Tsunduma Yajin Aiki

A ranar Litinin, 21 ga watan Satumba, 2020, kungiyar NARTO ta direbobinn motocin Najeriya, ta bada sanarwar za ta shiga yajin aiki a yau Talata.

Kungiyar direbobin su na da hannu wajen jigilar mai da fasinjoji da kuma kaya a kan hanyoyin Najeriya da kuma sauran kasashen Afrika ta yamma.

Shugaban NARTO na kasa, Alhaji Yusuf Lawal Othman, ya zanta da manema labarai jiya, inda ya shaida masu dalilinsu na tafiya wannan yajin aiki.

Da ya ke magana da ‘yan jarida a garin Abuja, Yusuf Lawal Othman, ya ce direbobin motocin haya sun yi mamakin jin labarin hana su bi ta kan tituna.

Jaridar The Nation ta bada ruhoton cewa kungiyar NARTO ta koka ne da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na haramtawa motoci masu cin lita sama da 45, 000 bin titi.

Shugaban kungiyar ya ce zasu fara yajin aikin a yau, 22 ga watan Satumba, 2020, domin su ja kunnen gwamnati. NARTO ta ce za ta bada wa’adin kwanaki 10.

Da zarar wannan wa’adi ya cika, kungiyar za ta janye aiki gaba daya har sai baba ta gani. Wannan wa’adi zai fara aiki ne daga ranar 24 ga watan Satumba.

Idan wannan ya faru, mutane da-dama za su rasa hanyar cin abinci, wannan ya sa tun farko kungiyar ta ja-kunnen gwamnatin Najeriya ta dauki mataki.

A cewar Alhaji Yusuf Othman, akwai rashin tausayi da rashin sanin ya kamata a matakin hana masu manyan motoci bin kan tituna duk da kokarin da su ke yi.

NARTO ta ce ta na taka rawar gani wajen kasuwanci da jigilar mai tsakanin jihohin kasar nan.

Labarai Makamanta