Kungiyar Arewa Ta Yi Watsi Da Kiran Korar Sakataren Gwamnatin Tarayya Daga Mukaminsa

Ƙungiyar dake rajin samar da zaman lafiya da ciyar da yankin Arewa gaba (Arewa New Agenda) ta yi tir gami da Allah wadai da kiran da wasu ke yi na a kori sakataren gwamnatin tarayya George Akume daga muƙamin sa.

Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwar da ta fitar wadda ta samu sanya hannun shugaban ta na kasa Sanata Ahmed Abubakar MoAllahyidi.

Sanarwar ta bayyana cewa “Hankalin Ƙungiyar ya kai bisa ga wani jawabi da Chif Audu Ogbe ya yi a wani taron manema labarai da al’ummar Idoma inda ya ke sukar nadin Akume kasancewar shi ya fito daga kabilar Tiv da cewar Idoma ba sa goyon bayan wannan matsayi da aka ba shi daga jihar Binuwai, inda suka bayyana hakan a matsayin danniya ga jama’ar Idoma.

Kungiyar ta cigaba da cewar al’ummar Idoma na da dama a mulkin dimokuraɗiyya kuma da ‘yanci na su fito su bayyana abin da ke zukatan su, amma hanyar da suka bi wajen isar da sakon zai jefa ‘yan Najeriya cikin rudani.

Sanarwar ta bayyana cewar zaben George Akume da akayi a matsayin sakataren gwamnatin tarayya ya samu karɓuwa a dukkanin fadin Najeriya saboda zabe ne da akayi shi cikin adalci da samun daidaito bayan kammala babban zaben shugaban kasa.

Kungiyar ta bayyana cewar zaben George Akume an yi shine domin samun wakilcin Arewa musamman Kiristocin Arewa a cikin Gwamnatin Tinibu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply