Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamnatin jihar ta yi karin haske kan dalilin da yasa ta garkame ginin ofishin Barista Nuraini Jimoh babban Lauyan tsohon Gwamnan Jihar Sanata Ibrahim Shekarau.
An ruwaito cewa Barista Jimoh, daya daga cikin lauyoyin Malam Ibrahim Shekarau da wasu ma’aikatansa an garkamesu na tsawon sa’o’i a cikin ofishinsa bayan umarnin gwamnatin Jihar karkashin Gwamna Ganduje.
A wata takarda da hukumar kula da gidaje ta fitar, ta ce gwamnatin ba ta lauyan ta ke ba sai dai ta mamallakin ginin. Murtala Shehu Umar, mai magana da yawun hukumar, ya kwatanta rahoton da zancen kawai inda ya kara da cewa an rufe gine-gine masu yawa a ranar.
“Gwamnatin jihar ta rufe gini mallakin Isiyaka Rabi’u & Sons a C14/C16 kan titin Murtala Muhammad ta karkashin kwamitin hukumar kula da filaye.” “Kwamitin ya mika takarda ga mai ginin a ranar 14 ga watan Satumba kuma an bashi wata daya da ya zo ya biya kudin harajin da ake bin shi tun daga shekarar 2016 zuwa 2021.
“Mun rufe a kalla gine-gine talatin a ranar 1 ga watan Disamba a sassan jihar. Wuraren sun hada da Zoo road, Zaria road da Ibrahim Taiwo road. “Hakazalika, an garkame wasu gini 7 da ke kan titin Murtala Muhammad bayan an mika takardar jan kunne tun wata daya da ya gabata amma ba su yi martani ba.
Don haka kwamitin zai cigaba da rufe duk wata kadara da mamallakin ta ya ki bin doka. “A matsayinmu na jami’an hukumar, takardu sun nuna cewa ginin mallakin Isiyaka Rabi’u & Sons ba Barista Nuraini Jimo ba. Damuwar mu ita ce mai ginin ba wai wanda ke haya ba,”