Kul! Da Korar Fulani Daga Jihar Ondo – Buhari Ga Gwamna

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta soki umarnin gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, na korar makiya daga dazukan Jihar Ondo.

Idan baku manta ba, gwamnan ya bawa kwana Bakwai da su bar dazukan jihar nan, daga ranar Litinin 18 ga Janairun 2021,” a cewar gwamnan.

A martanin ta ranar Talata, fadar shugaban kasa ta bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya ce Mr Akeredolu, babban lauya, “ba za a tsammaci ya kori dubban makiyan da rayuwar su ta dogara da jihar ba bisa yan ta’addan da suka mamaye daji ba.

“Gwamnatin Ondo, da sauran 35 na kasar nan dole ne su dinga bambance yan ta’adda da kuma yan kasa masu bin doka wanda suma dole ne a kare rayukan su. Karkashin doka da oda, yaki da ta’addanci yaki ne na ceto kimar dan Adam wanda ya rataya a hannun kasar mu.”

Fadar shugaban kasar ta kuma bayyana bukatar da ke akwai na rashin danganta yanki, kabila ko addini da laifuka ko ta’addanci sai dai a ware laifin gefe guda a magance shi.

Labarai Makamanta