Tsohon gwamnan Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi ya yi kira ga mutanen Kudancin Kaduna su guji tashin hankali su rungumi sulhu.
Tsohon gwamnan ya nuna rashin jin dadin sa game da sake ɓarkewar rikici a yankin cikin sanarwar da kakakinsa Mukhtar Zubairu ya fitar ranar Juma’a. Ya ce daukan doka a hannu don nuna bacin rai ƙara dagula lamura ya ke yi ba kawo maslaha ba.
“Na yi imani cewa tattaunawa da juna ce hanya mafi dacewa na samar da tabatattaciyar zaman lafiya da fahimtar juna wacce ke kawo cigaba. “A game da rikicin da ke faruwa a yankin, ya yi kira ga al’ummar su rungumi tattaunawa da juna da sulhu duk yadda ake ganin da wahala,”
Ya kuma yi kira ga mutanen yankin su ba gwamnati haɗin kai da goyon baya don magance wannan ƙallubalen. Sanata Makarfi ya kuma yi kira ga gwamnatin jiha da ta tarayya su tabbatar an tura isasun jami’an tsaro don samar da tsaro a yankin duba da cewa ana zargin wasu daga waje ne ke kai harin.
Ya shawarci hukumomi musamman gwamnatin jihar ta mayar da hankali wurin warware matsalar baki ɗaya ta hanyar neman hadin kan masu ruwa da tsaki kamar masu sarautar gargajiya da shugabannin addini, ƴan siyasa da shugabannin al’umma.